Harin ƙunar baƙin wake a Kamaru | Labarai | DW | 29.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ƙunar baƙin wake a Kamaru

Aƙalla mutane guda biyar suka mutu a cikin wasu tagwayen hare-hare na kunar baƙin wake a Yankin arewa mai nisa na Kamaru.

Wasu mata ne guda biyu suka kai hare-haren a garin Dabanga da ke a yankin Arewa mai nisa na ƙasar.Gwamnan Yankin na arewa mai nisa Midjinyawa Bakary ya sanar da cewar ɗaya daga cikin matan,ta tayar da bam ɗin ne a cikin wani gidan iyalai, yayin da ɗaya ta tarwtsa kanta a cikin wani shago.

Ya zuwa yanzu ba a da masaniya dangane da waɗanda ke da alhakin kai harin. Sai dai ana kyautata zaton cewar Ƙungiyar Boko Haram ce ke da alhaki, saboda ta yi kaurin suna a wannan fanni.