Harin ƙunar baƙin wake a Iraƙi | Labarai | DW | 07.12.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ƙunar baƙin wake a Iraƙi

Akalla mutane 16 suka rasa rayukansu kana wasu 27 suka jikkata ,waɗanda suka hadar da shugabannin kabilu ,da masu da mayakan sakai ,mata da yara ,sakamakon wani harin kunar baƙin wake a gunduwar Diyala dake ƙasar Iraki.

Wata mace ɗauke da jigidar boma bomai ta aiwatar da wannan harin ,da safiyar yau a cikin harabar inda ake gudanar da taron majalisar ‚yan sunni ,a tsakiyar garin Muqdadiya.Waɗanda suka hganewa idanunsu sun shaidar dacewar,’yar kunar bakin waken da shiga offishin ne da sunan ganawa da shugaban taron.Majalisar ‚yan sunnin dai ,na mai zama wani komiti ne na wakilan ƙabilu da mayakan sakai ,waɗanda ke taimakawa jami’an tsaron Irakin ,wajen yakar mayakan tarzoma a ƙasar.

 • Kwanan wata 07.12.2007
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CYnG
 • Kwanan wata 07.12.2007
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/CYnG