Harin ƙunar baƙin wake a Afganistan | Labarai | DW | 17.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ƙunar baƙin wake a Afganistan

Mutane uku suka mutu kana wasu 22 suka jikkata a cikin harin da aka kai a birnin Kabul.

Hukumomi a birnin Kabul na Afganistan sun ce mutane uku suka mutu a cikin harin wanda aka kai a kusa da filin saukar jiragen sama na birnin.

A ciki har'da wani dan ƙasar Birtaniya wanda ke yin aiki tare da wata tawagar 'yan sanda na Ƙungiyar Tarraya Turai da kuma wasu 'yan matan guda biyu.
Harin wanda wani ɗan kunar baƙin wake ya kai shi da wata motar ɗauke da bama-bamai,tuni da Ƙungiyar Taliban ta yi ikiran ɗaukar alhakin kai shi a shafinta na Twiter.