Hari ya rutsa da ′yan sanda a Afghanistan | Labarai | DW | 30.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya rutsa da 'yan sanda a Afghanistan

Mahakumta a kasar Afghanistan sun sanar da rasuwar wasu 'yan sanda sabin dauka sakamakon wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake a yammacin birnin Kabul.

Afghanistan Selbstmordanschlag in Kabul

Harin kunar bakin wake da aka Kai a birnin Kabul

A cikin wani hari ne dai da aka kai wa ayyarin motoci 'yan sanda sabin dauka a wata unguwa mai cinkoson jama'a a da ke yammacin birnin na Kabul, 'yan sanda a kalla 27 suka mutu, tare da raunata wasu 40 a cewar wani jami'in ofishin ma'aikatar ministan cikin gidan kasar ta Afghanistan. Cikin wata sanarwa da ya fitar bayan harin, kakakin masu kai harin Zabihullah Mujahid, ya tabbatar cewa maharan na su sun kai hari ga motocin bus-bus guda biyu, kuma sun hallaka mutane da dama.

Shaidun gani da ido sun ce bayan tarwatsewar bam na farko, sai kuma ba da jimawa ba bam na biyu ya tashi a daidai lokacin da ake kokarin zuwa da sabin 'yan sandan wajen ayyukan horo.