Hari ya kashe mutane shida a Somaliya | Labarai | DW | 26.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya kashe mutane shida a Somaliya

Kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin bam na mota da wasu 'yan bindiga suka kai, a wani wurin cin abinci a birnin Mogadishu na Somaliya.

A kalla mutane shida ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai a birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar Somaliya. Wasu 'yan bindiga ne suka kai harin a wata mota da aka dasa bam a cikinta a wani wajen cin abinci da maraicen Alhamis.

Rahotanni daga kasar na nuni da cewar an kuma ta yin musayar wuta tsakanin 'yan bindigar da jami'an tsaro.'Yan sanda sun ce an harbe biyu daga cikin maharan, yayin da aka ji wa guda rauni kuma tuni aka kama shi.

Masu tada kayar baya na kungiyar Al-Shabaab sun dauki alhakin harin na birnin na Mogadishu.