Hari ya jawo hana sallar Juma′a a Jerusalem | Labarai | DW | 14.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya jawo hana sallar Juma'a a Jerusalem

Wata kafar yada labaran rediyo ta soja ta bayyana cewa harin an kai shi ne kusa da wurin ibada da Musulmi da Kirista ke zuwa.

Wasu mahara su uku sun bude wuta a kusa da wurin ibada mai tsarki a birnin Jerusalem a ranar Juma'a inda suka raunata wasu 'yan Isra'ila su uku biyu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali kafin daga bisani 'yan sanda na Isra'ila suka aika da maharan lahira.

Wata kafar yada labaran rediyo ta soja ta bayyana cewa harin an kai shi ne kusa da wurin ibada da Musulmi da Kirista ke zuwa.

A cewar Magen David Adom da ke aiki da motar daukar marasa lafiya a Isra'ila biyu daga cikin 'yan Isra'ila da maharan suka harba rayuwarsu na cikin hadari babba don haka ake basu kulawa ta musamman. 'Yan sanda dai sun bada umarni na hana sallar Juma'a a wannan wurin ibada saboda harin.

Dubban al'umma ne dai ke gabatar da sallar Juma'a a masallacin Kudus wurin ibada na uku mafi girma da Musulmi ke ibada a duk rana irin ta yau.