Hari ya hallaka fiye da mutane 30 a Najeriya | Labarai | DW | 12.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya hallaka fiye da mutane 30 a Najeriya

Bama-bamai biyu sun fashe a wuri mai cike da mutane a garin Jos da ke yankin tsakiyar kasar

Wasu bama-bamai biyu da suka fashe a garin Jos na Jihar Plato da ke yankin tsakiyar Najeriya sun hallaka fiye da mutane 30, tare da jikkata wasu masu yawa, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma ana dangantawa da kungiyar Boko Haram wadda ta yi kaurin suna wajen kai hare-haren da ke hallaka mutane cikin yankin arewacin kasar.

Boko Haram ta karbe wasu yankuna da ta ayyana kafa daular Islama, inda 'ya'yan kungiyar ke ci gaba da fafatawa da dakarun kasar ta Najeriya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu