Hari ta sama ya kashe mutane 16 a Yemen | Labarai | DW | 31.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ta sama ya kashe mutane 16 a Yemen

Majalisar Dinkin Duniya ta kirayi masu sa ido na kasa da kasa da su binciki yadda fararen hula ke rasa rayukan su a kasar Yemen.

Mutane 16 sun mutu ciki har da mata da kananan yara a wani harin da jiragen saman yaki suka kai a kan gidajen fararen hula a lardin Sahan Cin Saada da ke arewa maso yammacin Yemen. Masu aiko da rahotanni sun bayyana cewa jiragen kawancen yaki da Saudiyya ke jagoranta ne suka kaddamar da wannan hari.

Tuni dai masu aiyyukan ceto ke ci gaba da tsamo gawarwaki daga gine-gine, yayin da wadanda harin ya ribta da su ke karban jinya daga jami'an kiwon lafiya.

Mai kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al Hussein, ya kirayi masu sa ido na kasa da kasa da su binciki yadda fararen hula ke rasa rayukan su a kasar Yemen. A wani rahoton da ya wallafa a makon da ya gabata Zeid Ra'ad Al Hussein ya nuna alkalumman fararen hula 2067 da suka salwanta tun lokacin da kasar Saudiyya ta shiga yaki a Yemen.