Hari kan ′yan sanda a birnin New York | Labarai | DW | 06.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari kan 'yan sanda a birnin New York

An harbi wasu 'yan sanda guda biyu a birnin New York na Amirka inda kuma tuni aka garzaya da su zuwa asibiti kamar yadda jami'an 'yan sanda suka bayyyana a daren jiya Litinin.

Ofishin 'yan sanda a birnin na New York ya bayyana cewa 'yan sandan sun sami raunika bayan harbin da suka samu na 'yan fashi da makami a yankin Bronx na New York.

Ofishin ya ce a yanzu babu cikakken bayani akan halin da 'yan sandan ke ciki, haka zalika babu wani cikin maharan da ya zo hannu. Babu kuma wasu karin bayanai da aka samu daga jami'an 'yan sandan.

Wannan harbi dai ga jami'an 'yan sandan na zuwa ne makonni bayan da wani bakar fata a birnin na New York ya hari wasu 'yan sanda ya halaka tare da kashe kansa, abinda ya bayyana a matsayin fansa ga kisan wasu bakaken fata a Amirka.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu