Hari kan wata jami′a a Kenya | Labarai | DW | 02.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari kan wata jami'a a Kenya

Rahotannin daga arewacin kasar Kenya na cewar wasu 'yan bindiga sun afakawa wata jami'a a birnin Garissa inda suka hallaka mutane da dama.

Mazauna yankin suka ce sun ji karar fashewar wasu abubuwa da ake kyautata zaton bama-bamai ne kana sun ce hayaki ya turnuke sararin samaniya a inda jami'ar ta ke.

Al-Noor Maulid wani dan jarida da ke zaune a birnin na Garissa ya shaidawa DW cewa mazauna yankin na ciki hankali kuma jami'an tsaro sun killace wajen.

Yanzu haka dai an ce yawan wanda suka rasu ya kai 14 kuma akwai yiwuwar yawansu ya karu. Kungiyar bada agaji ta Red Cross ta ce an jikkata mutanen da yawansu ya tasamma 30.

Arewacin Kenya da ke da iyaka da Somaliya dai na ya sha fama da hare-hare na 'yan bindiga makamancin wannan, galibinsu daga kungiyar nan ta al-Shabab da ke da alaka da kungiyar al-Qaida.