1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari kan soji a Afghanistan

Yusuf BalaOctober 2, 2014

Amirka da ƙawayenta na Ƙungiyar tsaro ta NATO na shirin ci gaba da aiyyuka a Afghanistan.

https://p.dw.com/p/1DOfO
Kabul Anschlag 01.10.2014
Hoto: Reuters/Omar Sobhani

Jami'ai sun bayyana cewar wani ɗan kunar baƙin wake da ya tashi kansa a wani harin kunar bakin wake, bayan hallaka kansa ya kuma kashe wasu jami'an soji uku, da raunata wasu bakwai a birnin Kabul kwana daya bayan da aka kai irin waɗannan hare-hare har sau biyu da suka yi sanadin kisan mutane 11. Hafeiz Khan da ke zama shugaban 'yan sanda a lardin ya bayyana cewar ɗan ƙunar bakin waken ɗaure da bama-bamai ya tashi bam ɗin ne a kusa da wata mota kirar bus da ta ɗauko sojoji a safiyar Alhamis ɗin nan kan hanyar su zuwa wurin aiki.