Hari kan Firimiyan Habasha
June 23, 2018Fashewar abin wanda ake kyautata zatan bam ne, inda a jawabin da ya yi wa 'yan kasar bayan kai harin, firaminista Abiy Ahmed, ya ce harin ya yi sanadin mutuwar mutane da yawa kana ya jikkata mutane sama da 83, ko da yake daga baya a shafin twitter shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin kasar ta Habasha, ya musun ta cewa akwai wadanda suka mutu. A cewar firaministan, wasu makiyan zaman lafiya ne suka kai hari, amma ba su yi nasara ba.
Wani ganau ya shaidawa Sashin Amharic na DW cewar ya ga mutane da damar gaske da suka jikkata, wanda aka kai su asibiti don yi musu magani kuma wasunsu na nan rai-kwakwai mutu-kwakwai, inda ya kara da cewa.
"Motar daukar marasa lafiya ta kwashi mutane da dama, da yawa daga cikinsu jina-jina kuma an kai su asibiti don yi musu magani. Wasu daga cikin wanda suka jikkatan na cikin mawuyacin hali. Mutane na ta kokarin sanin abinda ya faru amma an ce mana bam ne ya tashi".