Hari da wuka kan sojoji a Brussels | Labarai | DW | 26.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari da wuka kan sojoji a Brussels

A kasar Belgiyam jami'an tsaro sun bindige har lahira wani mutun da ya kai hari da wuka kan sojoji a yammacin jiya Jumma'a a tsakiyar birnin Brussels a daidai lokacin da sojojin ke aikin sintiri.

A kasar Belgiyam jami'an tsaro sun bindige har lahira wani mutun da ya kai hari da wuka kan sojoji a yammacin jiya Jumma'a a tsakiyar birnin Brussels a daidai lokacin da sojojin ke aikin sintiri na rigakafin afkuwar harin ta'addanci da birnin ke yawan fuskanta a baya bayan nan. 

Kafofin yada labarai na kasar sun bayyana cewa mutuman da ya kai harin dan asalin kasar Somaliya ne mai shekaru kimanin 30. Tuni dai hukumomin shari'a na kasar ta Beljiyam suka bayyana harin a matsayin na ta'addanci. 

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa sai da mutuman ya yi kabbara kafin ya afka wa sojojin wadanda su kuma nan take suka buda musa wuta.