Hari da gurneti ya hallaka mutane 16 a Kenya | Labarai | DW | 23.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari da gurneti ya hallaka mutane 16 a Kenya

'Yan sanda sun ce, an kwashe watanni ana zaman zullumi saboda sabani tsakanin wasu kabilu biyu na yankin.

Kimanin mutane 16 sun hallaka sakamakon hari da gurneti cikin yankin arewa maso gabashin Kenya, kusa da iyaka da kasashen Somaliya da Habasha. Kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa wato Red Cross, ta ce kuma akwai wasu mutane fiye da 20 da suka samu raunika.

'Yan sanda sun ce, an kwashe watanni ana zaman zullumi saboda sabani tsakanin wasu kabilu biyu na yankin. Kuma wannan hari ya faru yayin da ake tattaunawa kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya cikin yankin.

Tun cikin watan Mayu gwamnatin Kenya, ta kara tura jami'an 'yan sanda zuwa yankin, sannan tana shirin tura sojoji, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu