1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a ofishin jakadancin China a Pakistan

Abdullahi Tanko Bala
November 23, 2018

'Yan kungiyar aware ta Balochistan ta yi ikrarin daukar alhakin harin ta'addanci a ofishin jakadancin China a Pakistan

https://p.dw.com/p/38lqS
Pakistan Angriff auf chinesisches Konsulat in Karachi
Hoto: Reuters/A. Soomro

Wasu 'yan kunar bakin wake su uku na wata kungiyar masu tada kayar baya a Pakistan sun kai hari karamin ofishin jakadancin China dake kudancin Karachi a ranar Juma'ar nan.

Wani mai magana da yawun kungiyar ya shaidawa kamfanin dillancin Labaran Reuters ikrarin cewa su 'yan kungiyar 'yantar da yankin Balochistan sune suka kai harin.

Akalla yan sanda biyu da kuma wani dogari daya sun rasa rayukansu a harin.

Babu tabbas ko akwai wani jam'in kasar China da harin ya ritsa da shi.

China  ta yi Allah wadai da harin tare da bukatar hukumomin Pakistan su tabbatar da tsaron lafiyar 'yan China da ke zaune a kasar.