1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a Najaf

Zainab A MohammadApril 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bu75
Wani bomb da aka dasa a wata mota ,ya tarwatse kusa da wurin bauta yan darikar shia a garin Najaf dake kudancin Iraki,wanda kawo yanzu mutane 15 suka rasa rayukansu banda masu yawa da suka jikkata.Wakilin kamfanin dillancin labarai daya ganewa idanunsa tarwatsewar Bomdi,yace yaga gawawwakin mutane 10,mitoci 100 daga wurin bauta na Imam Ali ,wanda ke zama mafi tsarki way an shai a duniya baki daya.Wannan harin na yau dai yazo ne adai dai lokacin da shugabanin Irakin ke kokarin kafa sabuwar gwamnati,watanni hudu bayan gudanar da zaben yan majalisar dokoki,batu da ake ganin cewa zai iya dada sabanin siyasa,daka iya rura wutan banbanci da kasar ke fama dashi na lokaci msai tsawo.Prime minista Ibrahim Jaafari dai na cigaba da fuskantar matsin lamba na sauka daga mukaminsa,domin samun sukunin nada sabuwar gwamnati.To sai dai Premiern yayi watsi da kiran da larabawa yan adawa na Sunni da kurdawa da ma wasumanyan shian kasar keyi na janyewa daga takara dayake yi a sabuwar gwamnatin.Wannan badi dai ya dada haifar da rarrabuwar kaweuna tsakanin yan shia dake da rinjaye a gwamnatin Irakin,wanda kuma keda goyon bayan yan yakin sunkuru dake cigaba da tayar da hankula a garuruwa,kamar Najaf.