Hari a kan wata gada da ke Gao na Mali | Labarai | DW | 08.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari a kan wata gada da ke Gao na Mali

Kungiyar Mujao ta tarwatsa wata gada a kusa da birnin Gao da ke arewacin Mali inda wasu mutane fararen hula suka jikata.

Masu kaifin kishin Islama na kasar Mali sun tarawatsa wata gada a kudancin yankin Gao a kusa da iyaka da Jamhuriyar Nijar. Wani kansela na garin Gao wato Ibrahim Cisse ya bayyana wa kanfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa wannan al'amarin dai yayi sandiyyar jikata fararen hula guda biyu. Shi dai Cisse ya ce masu kaifin kishin Islaman sun zo kan wani babur a lokacin da suka tarwatsa daya daga cikin gadojin na wannan kauye.

Rundunar 'yan sanfan Mali ta bayyana cewar masu kaifin kishin addinin sun yi niyar tarwatsa tagwayen gadojin da ke garin da ke kusa da Gao, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba. Wannan harin ya zo ne kwana daya bayan kai wasu hare- hare da mayan bindigogi a yankin na Gao da ke Arewacin Mali. Tuni dai kungiyar MUJAO ta dauki alhakin kai wannan harin, tare da barazanar kai wasu karin hare-hare.

Mawallafi: Youssoufou Abdoulaye
Edita: Umaru Aliyu