Hari a kan jami′an jandarma a Mali | Labarai | DW | 20.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari a kan jami'an jandarma a Mali

Wasu 'yan bindiga dadi sun kai hari a kasar Mali tare da halaka jami'an jandarmomin kasar uku.

Jami'an tsaron Mali na fuskantar kalubalen hare-hare

Jami'an tsaron Mali na fuskantar kalubalen hare-hare

Wasu 'yan bindiga dadi sun kai hari kasar Mali tare da halaka mutane da dama. Wani shaidan gani da ido Moussa Saye ya ce maharan sun hallaka jami'an jandarma na kasar guda uku a yankin tsakiyar Mali. Saye wanda ke da zama a garin Mopti, ya ce ya na da 'yan uwa da ke zaune a kusa da inda aka kai harin na wannan Laraba. Dakarun kasar ta Mali sun tabbatar da faruwar harin, wanda suka ce dama yankin ya yi kaurin suna wajen samun tashe-tashen hankula daga tsagerun kungiyar "Macina Liberation Front", da ke da tsautsauran ra'ayin addini, wada kuma ta dauki alhakin kai hare-hare da dama cikin shekarar da ta gabata.