Hari a birnin Leicester na Birtaniya | Labarai | DW | 26.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari a birnin Leicester na Birtaniya

Hukumomi a Birtaniya sun ce fashewa tare da rushewar wani gini da suka jikkata mutum shida a birnin Leicester na kasar, bashi wata alaka da harin ta'addnci.

'Yan sanda a Birtaniya, sun nesanta fashewa tare da rushewar wani gini da suka jikkata mutum shida a birnin Leicester da alaka da ta'addnci. Da maraicen Lahadi ne dai fashewar ta auku a kan titin birnin da ke cike da gidaje gami da zirga-zirgar jama'a. Lamarin ya tilasta yanke wutar lantarki a gidaje da dama saboda bai wa jami'an agaji damar kai dauki.

Jami'an 'yan sanda da na kwana-kwana, sun ja hankalin kafofin watsa labarai da su guji karin gishiri kan lamarin, musamman ma alakanta shi da ta'addancin. Jami'an sun kuma ce suna ci gaba da gudanar da bincike, kuma nan gaba kadan za su sanar da cikakken abin da ya auku.