Hare-haren Boko Haram na karuwa a Najeriya | Siyasa | DW | 19.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hare-haren Boko Haram na karuwa a Najeriya

Rayuka na kara baki fata kuma na kara shiga duhu a cikin yankin arewa maso gabashin Tarrayar Najeriya da ke fama da karin hare-haren kungiyar Boko Haram

Babu dai zato ba kuma tsammani aka bada labarin sace wasu 'yan mata sama da 100 a garin Gumsuri da ke makwabta da dan uwansa da ke Chibok a wani abin da ke zaman alamun sake ta'azzarar hare-haren 'ya'yan kungiyar Boko Haram da ke dada tasiri yanzu haka.

Sabon harin da ko bayan satar 'yan matan ya kai ga kisan mutane kusan 40 dai na zuwa ne a dai dai lokacin da rundunar sojan kasar take fadin tai nisa a kokari na ganin bayan kungiyar.

Abun kuma da daga duk alamu ke nuna irin banbancin da ke akwai a tsakanin kalaman mahukuntan na Abuja da kuma zahirin da ke kasa a cikin yankin da ke dada komawa filin daga yanzu haka. Sanata Ahmed Zanna da ke wakiltar jihar Borno a majalisar dattawan kasar ya ce 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kaddamar da sabon hari a bisa garin Damboa dake zaman daya a cikin manyan garuruwan jihar.

An dai kame 'yan mata na Gumsurin ne a lokacin da mahukuntan na Abuja ke fadin har yanzu da sauran fata ga kokari na ceto takwarorinsu na Chibok da kuma ke neman share shekara guda a hannu Boko Haram.

Sauti da bidiyo akan labarin