Hare-haren bama-bamai a Iraki | Labarai | DW | 17.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren bama-bamai a Iraki

Mutane 15 suka mutu a harin na ƙunar baƙin wake da aka kai a yankin arewacin ƙasar.

An ba da rahoton cewar wani dan ƙunar baƙin waken da ke tuƙa wata motar maƙare da bama-bamai ya tayar da ita a arewancin Iraki inda ta tarwatse ta kuma kashe rayuka. 'Yan sanda sun ce mutane aƙalla guda 15 'yan ƙabilar Chabaks suka rasa rayukansu a cikin hare-haren da aka kai yayin da wasu da dama suka jikata a garin Muafakiya da ke cikin lardin Ninive.

A cikin watan jiya ma wasu hare-haren da aka kai a lokacn wata jana'izzar a garin an kashe mutane 21.Wata ƙungiya ta Iraq Body ta ce a shekara bana an kase sama da mutane dubu 60 a cikin tashin hankali da ake yi tsakanin ma'abiya aDdinin shi'a da 'yan Sunni a Iraki.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita :Mouhamadou Awal Balarabe