1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Amirka ta sama na tasiri kan kungiyar IS

Pinado Abdu WabaOctober 8, 2014

Rahotanni sun ce kungiyar IS ta fara komawa baya daga garin Kobane da ta kame a karshen makon da ya gabata bisa karfin luguden wutan da ake mata.

https://p.dw.com/p/1DS7L
Syrien Kobane IS Terror Grenze Türkei 8. Oktober
Hoto: Reuters/Murad Sezer

Hare-hare ta sama da Amirka ke jagoranta sun yi nasarar tura mayakan Siriya baya zuwa garin Kobane, garin Kurdawan Siriya da ke kan iyaka, wanda da suka yi niyyar mamayewa bayan da suka yi makonni uku suna kai hari, kamr dai yadda jami'an Kurdawa suka bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

Wannan gari dai na daukar hankalin al'ummar kasa da kasa tun bayan da kungiyar ta IS ta koro akalla mutane dubu 180 daga mafi yawan yankunan Kurdawa, abinda ya tilasta musu zuwa Turkiyya, abinda ya fusata Kurdawan Turkiyyan har su ma suka fara sanya baki.

Daga farkon wannan makon ne kungiyar IS ta sanya tutarta daga yankin gabashin kasar kuma tun daga wannan lokacin ne Amirka tare da tallafin kasashen larabawa na yankin Gulf, da ke adawa da akidun kungiyar ta IS suka ribanya hare-harenta ta sama