Hare haren ƙunar baƙi wake a Syriya sun laƙume rayukan jama′a. | Labarai | DW | 21.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare haren ƙunar baƙi wake a Syriya sun laƙume rayukan jama'a.

Mutane a ƙalla guda 30 suka mutu yayin da wasu da dama suka sami raunika,sakamakon fashewar wani abin a kusa da cibiyar jam'iyyar Baas a Damascus.

Gidan telbijan na ƙasar ta Syriya ya sanar da cewar bayan wannan hari da ake kyautata zaton cewar yan ta'ada ne suka kai shi.Wasu rokoki guda biyu da aka harba sun faɗa kusa da cibiyar rundunar sojojin ƙasar.

A share ɗaya kuma ƙungiyar yan adawa na ƙasar ta Syriya ta CNS, na can na gudanar da wani traro a birnin Alƙahira na ƙasar Masar domin samin mafita a rikicin na Syriya.Sai dai tuni a cikin wani shirin sanarwa da ƙungiyar zata baiyana ta yi gargaɗin cewar ba za a iya haɗa shugaba Bashar Al -Assad a cikin wata yarjejeniyar da za a cimma ba.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu