Hare haren ƙunar baƙi wake a Najeriya | Labarai | DW | 28.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare haren ƙunar baƙi wake a Najeriya

Wani dan kunar bakin wake ya kai hari akan wata coci da ke a garin Kaduna da ke a yanki arewaci na ƙasar

Mutane da dama ne suka mutu a cikinsu har da wanda ya kai harin yayin da wasu suka samu raunuka; a sa'ilin da wani abu mai ƙarfin gaske ya fashe a cikin cocin a lokacin da wasu kristocin ke yin ibada da suka saba yi a ranar lahadi.

Wani kakakin hukumar agajin gauggawa ta Nema ya gaya wa manema labarai cewar wanda ya kai harin ya darkaka cikin cocin da wata motar da ke maƙare da bama bamai .Yan sanda, sun ce mutane ukku suka mutu a harin, to amma waɗanda abin ya faru a kan idanunsu sun ce asarar rayukan na da yawa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas