Hare-hare sun yi sauki a Ukraine | Labarai | DW | 02.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare sun yi sauki a Ukraine

Rundunar sojojin kasar Ukraine ta sanar da mutuwar wani sojanta guda yayin da wasu hudu kuma suka jikkata a yayin wata bata kashi da 'yan aware.

Wannan dai na nuni da cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba a kokarin ganin an tabbatar da amfani da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan awaren gabashin kasar da ke goyon bayan Rasha, duk kuwa da cewa akwai tabbacin da ke nuni da cewa 'yan awaren na ci gaba da janye mayakansu da kuma makamansu daga filin daga. A cewar bangaren gwamnatin ta Ukraine an ma samu sassaucin kai hare-hare daga bangaren 'yan awaren, sai dai sunyi gargadin cewa akwai yiwuwar 'yan awaren na janyewa ne domin sake hada karfinsu waje guda kan su dawo su farwa dakarun gwamnatin. A kallah mutane 6000 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu cikin rikicin na Ukraine a kasa da shekara guda.