Hare-hare sun hallaka mutane 50 a Iraki | Labarai | DW | 10.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare sun hallaka mutane 50 a Iraki

Hare-haren bama-bamai cikin wasu yankunan birnin Bagadaza sun hallaka kimanin mutane 50 a Iraki.

Wasu jerin hare-haren da aka kai da bama-bamai, cikin yankunan galibin Musulmai mabiya darikar Shia, sun hallaka kimanin mutane 50 a Bagadaza babban birnin kasar Iraki.

Jami'ai sun ce akwai kimanin wasu mutanen 200 da suka samu raunika. Kuma an kai hare-hare wuraren shan shayi da kasuwanni, yayin da Musulmai ke bikin karamar Sallah, bayan kammala azumin watan Ramadan.

A ranar Talata wasu mutanen kimanin 31 sun gamu da ajalinsu yayin tashin bama-bamai a birnin na Bagadaza da ke zama cibiyar kasar ta Iraki. Kasar ta Iraki tana kara fuskantar rarrabuwar kai tsakanin al'ummar kasar, musamman 'yan Shia masu rinjaye wadanda ke rike da madafun iko, da kuma 'yan Sunni marasa rinjaye.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal