Hare-hare sun hallaka mutane 30 a kasar Iraki | Labarai | DW | 23.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare sun hallaka mutane 30 a kasar Iraki

Kasar iraki tana ci gaba da fuskantar hare-hare daga kungiyoyi masu dauke da makamai

Wasu jerin fashe-fashen bama-bamai da aka samu a kasar Iraki sun hallaka mutane masu yawa. Kafofin yada labarai sun ruwaito tashin bam a babban birnin Lardin Kurdana na Arbil, ya hallaka mutane yayin da wasu masu yawa suka jikata, lardin da ke da kwarya-kwaryar zaman lafiya. Sannan tashin wani bam a garin Kirkuk ya hallaka mutane 10.

Jami'ai sun ce mutane takwas sun hallaka sakamakon tashin wani bam a helkwatar hukumar tsaro da ke birnin Bagadaza fadar gwamnatin kasar ta Iraki.

A wani labarin kasar Katar ta yi kakkausar suka kan kungiyar da ke neman kafa daular Islama a Iraki, wadda ta ce suna aikata abubuwa irin na lokacin jahiliya. Ministan harkokin wajen kasar Khaled al-Attiyah ya musanta samar wa kungiyar tsagerun da kudade.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba