Hare-hare sun hallaka masu yawa a Najeriya | Labarai | DW | 27.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare sun hallaka masu yawa a Najeriya

Fiye da mutane 30 sun hallaka sakamakon hare-hare da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram a yankunan arewacin Najeriya

Fiye da mutane 30 sun hallaka sakamakon hare-haren bama-bamai da aka kai a yankin arewacin Najeriya, sa'oi kadan bayan gwamnati ta bayyana samun gagarumin nasara kan yaki da tsagerun 'yan ta'addan na kungiyar Boko Haram masu kaifin kishin addinin Islama.

Kimanin mutane 21 sun hallaka sakamakon tagwayen bama-bamai da aka tayar a garin Jos fadar gwamnatin Jihar Plato, a yammacin wannan Alhamis da ta gabata. Tun farko wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 23 a garin Biu na Jihar Borno. Gwamnatin kasar ta Najeriya ta ce sojojin kasar sun kwace garuru 10 daga hannun kungiyar Boko Haram.