1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane bakwai sun halaka a Mali sakamakaon hare-hare

Suleiman Babayo
July 12, 2019

Wasu hare-haren 'yan bindiga a yankin arewa maso gabashin Mali sun halaka mutane bakwai yayin da wasu 45 suka jikata.

https://p.dw.com/p/3M09c
Mali M'Pentièrébougou Dorf Ziegen
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Bätz


Wasu hare-hare biyu na 'yan bindiga a yankin arewa maso gabashin kasar Mali sun janyo mutuwar mutanje bakwai kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Nijar. 'yan siyasa da majiyoyin tsaro sun ce kimanin 'yan bindiga dadi shida suka kai hare-hare a wannan Alhamis da ta gabata.

Tun shekara ta 2012 kasar ta Mali da ke yankin yammacin Afirka ta tsunduma cikin rikicin kungiyoyin masu kaifin kishin addinin Islama, wadanda suka mamaye arewacin kasar kafin daga bisani sojojin faransa suka tainaka aka fatattaki tsagerun a shekara ta 2013. Tuni rikice-rikice suka fadada zuwa kasashe makwabta na Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.