1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare kan sarakunan gargajiya a Borno

May 30, 2014

Sarkin Gwoza, Alhaji Idrissa Timta, ya rasu bisa dalilin buuon zuciya, sakamakon harin 'yan bidiga a kan tawagoginsu bisa hanyar su ta zuwa Gombe.

https://p.dw.com/p/1C9VU
Mali Soldaten zwischen Markala und Niono 22. Januar 2013
Hoto: ERIC FEFERBERG/AFP/Getty Images

Wasu 'yan bindiga da ba'a kai ga sanin ko su waye ba sun kai hari ga wata tawagar Sarakunan yanka biyu wato Sarkin Gwoza Alhaji Idrissa Timta da na Uba Alhaji Ali Ibn Ismaila Mamza a jihar Borno, akan hanyar su ta zuwa jana'izar marigayi sakin Gombe.

Bayanai da ke fitowa daga yankin wanda ba na gwamnati ba, sun nunar cewa Allah ya yiwa Sarkin Gwoza rasuwa sanadiyyar bugun zuciya, yayin da shi Sarki Alhaji Ali Ibn Ismaila Mamza na Uba, ya kubuta daga hannun 'yan bidigar kuma yana nan cikin koshin lafiya a cewar dangin sa. 'Yan bindigar dai, sun yi kwanton bauna ne ga tawagar sarakunan a kauyen Zur da ke kusa da Shafa, a karamar hukumar Hawul ta jihar Borno..

Rahotannin kuma sun nuna cewa, an yi awun gaba da ‘yan Majalisar sarakunan da kuma fadawan dake cikin tawagar, sannan an kona motoci da dama.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaiwa tawagar sarakunan hari, inda kuma gwamnati ko jami'an tsaro ba su ce komai ba kan wannan hari ya zuwa yanzu ba.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar