1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare kan bakin haure ya ragu a Jamus

Yusuf Bala Nayaya
December 29, 2017

A shekarar ta 2017 an kai hare-hare sama da sau 1000 ga bakin haure sabanin sama da sau 3000 a shekarar 2016, kamar yadda rahoton masu fafutika ta kare baki a kasar ya nuna.

https://p.dw.com/p/2q5fs
Grenze Österreich Italien - Flüchtlinge Brenner Bahnhof
Jamus dai ta mamayi kafafan yada labarai saboda yawan baki da suka shiga kasarHoto: picture-alliance/dpa/J. Groder

Yawan kai hare-hare kan bakin haure ya ragu a Jamus a wannan shekara ta 2017. Wata kididdiga da aka fitar a jiya Alhamis wanda cibiyar Amadeu Antonio mai fafutikar kare hakkokin bakin haure ta ce an samu aikata laifuka sau 1,713 a wannan shekara adadin da za a ce ya ragu sosai idan aka kwatanta da cin zarafin 'yan gudun hijirar sau 3,768  da aka samu a shekarar 2016.

Shi ma dai ofishin da ke binciken aikata miyagun laifuka a Jamus (BKA) ya bayyana cewa an samu raguwa ta aikata miyagun laifuka kan 'yan gudun hijirar sai dai zai fitar da rahotonsa ne na shekarar 2017 a karshen watan Janairu na sabuwar shekara.

Ita kuwa magana da yawun ofishin na BKA ta fadawa kamfanin dillancin labaran Jamus dpa cewa zuwa ranar hudu ga watan nan na Dismaba an samu rahoto na kai hari sau 264 sabanin sau 995 da aka gani a shekarar 2016 kawo irin lokacin.