Hare-hare a Somalia | Labarai | DW | 10.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a Somalia

Yan takife a ƙasar Somalia sun kai wani saban hari gurneti,a babbar kasuwar birnin Modadiscio inda anan take mutane 2 su ka rasa rayuka sannan wasu da dama su ka ji raunuka.

Cemma a jiha litinin wani hari makamanci wannan ya rutsa da kasuwar, inda mutane 3 su ka kwanta dama.

Tashe tashen hankulla na daɗa tsamari a Somalia,tun bayan kiffar da gwamnatin dakarun kotunan Islama, yau da wattani 6 da su ka wuce.

A halin yanzu, gwamnatin riƙwan ƙwarya ta ƙara tsautarara matakan tsaro a birnin Mogadiscio a shirye-shiryen taron haɗin kann ƙasa, da da za a fara ranar lahadi mai zuwa.

A ɗaya wajen,hukumar kulla da yan gudin hijira ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ta bayana rahoto a game da mutanen Somalia da su ka rasa rayuka, kokuma su ka yi kasa ko sama, a yayin da su ka buƙaci shiga ƙasar Yamal ta jiragen ruwa.

A jimilce, rahoton ya ce daga farkon shekara ta da mu ke ciki zuwa yanzu, mutane 300 su ka mutu cikin ruwa a yayin da kussan 120 su ka ɓata a yunƙurin su na zuwa Yamal, da zumar kauce wa tashe-tashen hankulla.