Hare-hare a Iraki sun hallaka mutane 15 | Labarai | DW | 14.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a Iraki sun hallaka mutane 15

Wasu jerin hare-hare na kunar bakin wake da aka kai a birnin Bagadaza sun yi sanadiyyar rasuwar kimanin mutane goma sha biyar da kuma jikkata wasu da dama.

Iraqis inspect the site of a suicide car bomb attack in the Al-Haq square in Samarra, a predominantly Sunni town north of Baghdad, on July 5, 2013. Attacks killed five people in town squares in Iraq, including four who died when a suicide bomber set off his vehicle rigged with explosives just before midday prayers. AFP PHOTO/MAHMOUD AL-SAMARRAI (Photo credit should read MAHMOUD AL-SAMARRAI/AFP/Getty Images)

Irak Anschlag in Samarra

Wani dan sanda da ya roki a sakaya sunansa ya ce an kai hare-haren ne gabannin lokacin buda baki a kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane biyar a Nasiryyah da wasu hudu a Karbala yayin da mutane shidda su ka gamu da ajalinsu a Musayyib.

Baya ga wannan, jami'an sun ce harin na yau ya girgiza garin Kut da Basra sai dai kawo wannan lokacin ba a tantance wadanda su ka rasu ko jikkata ba.

Jama'a da dama a kasar dai na ta dari-dari dangane da yawaitar hare-hare makamantan wannan, inda wasu ke tunanin kasar ka iya komawa yakin basasa da ta tsinci kanta a ciki a shekarun 2006 da 2007.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohamed Abubakar