Hare-hare a garin Gao na kasar Mali | Labarai | DW | 07.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a garin Gao na kasar Mali

Rahotanni daga kasar Mali na cewar da sanyin safiyar yau an kai hare-hare na bam a garin Gao da ke arewacin kasar wanda ya yi sanadiyyar lalata gine-gine da jikkata wani soja.

Mai magana da yawun rundunar hadin gwiwa ta sojin Mali da Faransa wanda suka yi aiki fatattakar masu kaifin kishin addini a Mali din ya ce garin Gao da ke arewacin kasar ya fuskancin hare-hare na bam a karon farko cikin watanni da dama.

Jami'in mai suna Hubert de Quievrecourt ya ce kimanin bam biyar aka jefa da sanyin safiyar yau a garin na Gao wanda biyu daga cikinsu suka fada wata unguwa ta fararen hula.

Kawo yanzu dai babu wani wani labarin asarar rayuka da aka samu sai dai mai Mr. Quievrecourt ya ce sojan gwamnatin Mali daya ya jikkata.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai harin sai dai mabiya kungiyar nan ta Al-Qaida a watannin da suka gabata sun karbe iko da garin kafi daga bisani a fatatake su.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe