Hare-hare a birnin Dhaka na Banlgadesh | Labarai | DW | 01.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a birnin Dhaka na Banlgadesh

An ba da rahoton cewar wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a kan wani otel wanda baki yan kasashen waje ke sauka a Dhaka babban birnin kasar ta Bangladesh.

Ya zuwa yanzu dai babu wani karin bayyani da aka samu dangane da wannan al'amari sai dai wasu shaidu sun ce sun ji karar bindigogi a otel din da ke a wata unguwar da ke da jami'an diplomasiya na kasashen waje da dama a birnin na Dhaka.

Ofishin jakadacin Amirka a bisa shafinsa na Twitter ya ce harin ya hada har da yin gakuwa da mutane.