Hare-hare a Afganistan | Labarai | DW | 17.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a Afganistan

Ƙungiyar Taliban ta yi awan gaba da wasu mutane a jajibirin zaɓen ´yan majalisa

default

Ƙungiyar Taliban ta kai hare-hare a Afganistan

   Ƙungiyar mayaƙan taliban a ƙasar Afganistan ta yi awan gaba da wasu mutane guda 19 a ciki hadda ɗan takara guda, a jajibirin zaɓen ´yan majalisun da za a gudanar a ƙasar a gobe asabar idan Allah ya kaimu

Mutanen waɗanda suka haɗa da ´yan siyasa da kuma wasu ma´aikatan hukumar zaɓen  an sace su ne a Bad-ghis yankin da ke a arewa maso yammacin ƙasar

Kimanin mutane miliyan goma ne ake sa ran zasu kaɗa ƙuri´a a zaɓen domin zaɓen wakilan ´yan majalisun na jirga 249

Sai dai a halin da ake ciki masu lura da al'amuran yau da gobe na hasashen cewa jama´a ƙalilan ne zasu fito saboda barazanar da ƙungiyar ´yan taliban ɗin ta yi na kai hare hare a runfunan zaɓen

Mawallafi: Abdourahman Hassane

Edita: Yahouza Sadissou Madobi