Harar: Cibiyar Musulumci mai daraja
Birnin na daga cikin birane hudu na Musulumci da suka fi daraja a duniya, Harar cibiyar musulumci ce a kasar Habasha kamar yadda za a gani a jerin wadannan hotunan.
Harar Jugol, birni mai dimbin tarihi
Larabawa 'yan ci-rani ne suka kafa birnin na Harar a yayin da suka yada zango a tsakanin karni na 10 zuwa karni na 13. Birnin na da kofofi biyar da ake iya shiga cikinsa. Ya kuma kasance babban birnin jihar 'yan kabilar Oromo, wadanda suneke da rinjaye a kasar Habasha. Birnin na yankin gabashin kasar. UNESCO ta saka shi cikin jerin wurare masu dimbin tarihi a duniya tun a shekara ta 2006.
Wurin ziyarar Musulmi
Harar na da masallatai kimanin 82 da kuma wasu wurin ibadu sama da 100. Masallacin Grand Jami shi ne mafi girma a birnin. Kaso daya cikin uku na al'ummar kasar Habasha Musulmi ne, wato Musulmin ne ke da rinjaye.
Masallacin Mata
Masallacin Jami ya kasance masallaci daya tilo da aka kebe wa mata wurin yin sallah domin samun damar gudanar da ibada tare da maza. Suna iya shiga cikin masallacin ta wata karamar kofa da ke daman ginin. Sai dai ba sabon abu ba ne a gansu suna salla a wajen masallacin. Akasarin masallatan kasar kanana ne, saboda haka sai suka kasance na maza zalla.
Birnin zaman lafiya
Akwai wasu coci biyu a cikin birnin, cocin Medhane Alem ce kadai Cocin Orthodox a birnin. Mazauna birnin Harar na alfahari da yadda kowanne addini ke da 'yancin walwala. A shekarar 2003, UNESCO ta karrama birnin da kyautar yabon zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai. Sai dai a shekarun baya-bayan nan, an sami 'yar hatsaniya kan batutuwan da suka shafi rabon fili da kuma wakilcin jam'iyyu.
Tsarkin mazhaba
Akwai abin al'ajabi game da wannan birni da ke tsugune da al'umma fiye da dubu 120. Abu na farko shi ne tasirin Sufaye. Daya daga cikin wurare masu daraja a birnin sun hada da kabarin Sheikh Abadir Umar ar-Rida al Harari daya daga cikin wadanda suka kafa birnin. Wurin hutawar jama'a ne da ake yawan gani suna amfani da aswaki.
Ganye mai daraja
A can baya ana amfani da ganyen khat wajen rukiyya, amma yanzu ana amfani da shi a kusan duk sassan kasar Habasha. Yankin na Harar ya kasance yankin da aka fi amfani da ganyen ake kuma safarar shi zuwa wasu wurare. Ganyen da ake taunawa domin maganin gajiya da rashin cin abinci ya na samar wa kasar kudin shiga fiye da kaso 70 cikin 100. Maza da mata na amfani da wannan ganyen.
Kasuwancin yadi
Kasuwancin yadi na daga cinkin abin da ke bunkasa tattalin arzikin Harar. Ana kiran layin da kasuwar ta fi ci da suna “Makina Girgir” a sakamakon karar kekunan dinki. Ana yawan samun cunkoson matan karkara da ke zuwa kasuwar. Idan suka sayi yadin da suke so nan take suke bai wa teloli su kalmashe ko su yi musu dinki mai saukin sakawa. Yaduddukan na da ban sha'awa da launuka daban-daban.
Kasuwar da ke ci kullum
Tun daga wayewar gari zuwa yammaci, al'ummar Oromo na tururuwa a kasuwar domin saye da sayarwa. Su kan kwashi sa'o'i suna tafiya a kasa ko kuma kan jakuna. Bayan sayar da hajarsu suna amfani da kudin wajen sayan tukwane ko kayan sawa ko kuma abinci domin amfanin iyali. Akwai fannin masu safarar kaya zuwa kasuwar Musulmi da kuma kayan saka kamshin abinci. Harar na alfahari da wadannan sana'o'in.
Kasuwancin Rakuma
Birnin na da tazarar kilomita kusan 40 da kasuwar Rakuma da ke ci sau biyu a mako. Kimanin Rakuma 200 ake sayarwa a duk ranar kasuwa. Darajar Rakumi daya na kai wa tsakanin Euro 500 ko Dalar Amirka 565. Masu sayan Rakuman kan kasance makiyaya da suka fito daga kasar Somaliya. Ana cin naman Rakuman ana kuma hawan su.