Har yanzu tsugune bata kare ba a kasar Venezuela | Siyasa | DW | 31.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Har yanzu tsugune bata kare ba a kasar Venezuela

'Yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben raba gardama da aka gudanar a Venezuela, sun kuma kira sabuwar zanga-zanga.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya yi ikirarin samun nasara a zaben da ya gudana ranar Lahadi na wakillan da za su duba sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar, zaben da 'yan adawa suka yi watsi da shi tare da kiran wata sabuwar zanga-zanga. Wasu kasashen waje ma sun soki lamarin na magabatan kasar ta Venezuela, inda Amirka ta ce ba za ta amince da sakamakon ba.

Tun farko dai 'yan adawar kasar kira suka yi da a kaurace wa zaben wanda suka ce ba komai ba ne illa yunkurin bai wa shugaba Maduro damar ci gaba da mulki alhali wa'adin mulkinsa zai kawo karshe a shekara ta 2019. Tashe-tashen hankulan da suka gudana a lokacin zaben sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 wanda hakan ya kai adadin wadanda suka mutu sakamakon zanga-zangar gabaki daya ya zuwa mutun 120 tun farkon soma zanga-zangar.

Yayin da yake magana a gaban dumbin magoya bayanshi, Shugaba Maduro ya mayar da martani ga masu sukar zaben.

"Mun ji wani mai magana da yawun Shugaban Amirka Donald Trump da ke daukar kanshi a matsayin wani sarki na cewa ba za su amince da wannan zabe na mu ba. To dan me za mu damu da abun da Donald Trump yake fadi. Abun kawai da muka damu da shi, shi ne wanda 'yan kasar Venezuela masu cikakken 'yanci za su fada."

Sabuwar majalisar za ta rubuta sabon tsarin mulki

Wakilan da yawansu ya kai 545 za su kama aiki tun daga ranar Laraba wanda kuma za su jagoranci kasar na tsawon lokacin da ba a kayyade ba. Ana ganin wannan majalisa za ta iya rushe majalisar dokokin kasar wadda 'yan adawa suke da rinjaye a cikinta, sannan ita ce ke da karfin sake rubuta sabon kundin tsarin mulki da zai canji wanda tsohon shugaban kasar marigayi Hugo Chavez ya sa wa hannu a shekarar 1999.

Hugo Chavez (Picture-alliance/dpa/epa/Miraflores Press)

Tsohon shugaban Venezuela Hugo Chavez a tsakiya da Nicolas Maduro a dama sai shugaban majsalisa Diosdado Cabello a hagu

Tuni dai Shugaba Maduro ya bada tashi shawara a cewarsa kan abu na farko da ya kamata majalisar ta yi.

"Me ku ke tsammani kan yadda ta kamata sabuwar majalisar jagorancin kasar ta yi da babban mai shigar da kara ta gwamnati? Kawo sauye-sauye da kuma saka dokar ta-baci kai tsaye, tare da daukar jagoranci na mashara'antu, wannan ita ce 'yar shawarata mai kunshe da ma'ana."

Uwargidan Shugaba Maduro, Cilia Flores, da na hannun damarsa Diosdado Cabello da kuma da dama daga cikin masu mara masa baya na daga cikin membobin wannan sabuwar majalisa da za ta rubuta tsarin mulkin kasar. Yawan wadanda suka fito a zaben ya kai kashi 41.5 cikin 100 ma'ana 'yan kasar fiye da miliyan takwas sun fito domin zaben a cewar hukumar zaben kasar, abin da Shugaba Maduro ya kira a matsayin zabe mai cike da tarihi.

Mulkin danniya ya rasa goyon baya

Sai dai a cewar Maria Corina wata kusa a bangaran 'yan adawa watsi ta yi da wannan mataki na shugaban kasa.

Venezuela Proteste (Imago/ZUMA Press/J. C. Hernandez)

'Yan adawa sun yi shelar gudanar da sabuwar zanga-zanga a fadin kasar

"Wannan shi ne tunani na Venezuela. Tunani da babu wanda zai kawar da shi. Kuma ina mai fada a bayyane cewa yanzu mun kama hanyar kawo karshen mulkin danniya. A yau munga cewa abu na karshe da wannan mulki na kama karya ya so samu, shi ne neman turba ta gaskiya, amma kash hakan ba ta samu ba domin sun rasa wannan goyon baya da suka nema."

Shi ma dai daga nashi bangare dan adawa Jose Olivares na kasar ta Venezuela tsokaci ya yi kan halin da ake ciki inda yake cewa.

"Wannan sun kasance masu aikata manyan laifuka. Shi yasa muka tsaya tsayin daka domin kare kai daga matsalar yunwa da al'umma ke fuskanta, da mulkin danniya, da mugun talaucin da al'ummar Venezuela ke fuskanta. Suna iya ji mana ciwo, ko su ragargaza mu, amma kuma su sani cewa ba za su taba samu mu yi musu biyayya ba, domin wannan fada ba zai kare ba, sai lokacin da muka ga bayan mulkin Nicolas Maduro."

Baya ma ga kasar Amirka, kasashe irin su Kolumbiya, Panama, Peru, Argentina, da Costa Rica, sun ce ba za su amince da sakamakon wannan zabe ba, inda suka yi kira ga mahakuntan na Venezuela da su dakatar da girka wannan sabuwar majalisa.

Sauti da bidiyo akan labarin