Har yanzu Hama Amadou na tsare | Siyasa | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Har yanzu Hama Amadou na tsare

A Nijar tsohon kakakin majalisar dokokin kasar, Hama Amadou ya shafe kwanaki a gidan kaso ba tare da alkali ya saurare shi ba, abin da ya sabawa doka.

Abin dake daukar hankalin jama'a a Jamhuriyar Nijar shi ne kama Hama Amadou, shugaban, tsohon kakakin majalisar dokokin kasar kuma shugaban jam'iyyar Lumana Afrika dake adawa, wanda ya ke tsare a gidan kason garin Filinge mai nisan kilo mita wajen 200 a arewacin birnin Yamai, tun juma'ar da ta gaba. Tuni dai masu fashin baki suka shiga yada bayanan yi masa sakin talala. Hama Amadun da hukumomi ke nema ruwa jollo tun wata Agustan 2015 Domin yana cikin jerin mutum wajen 32 da ake tuhumar su da lafin badakalar cinikin jarirai.

Mutane sama da 30 ne suke cikin wannan badakalar ta cinikin jarirai, wadanda su kuma suak shafe watanni shidda suna tsare, kafin alkalin kula da bincike ya kammala bincike, a kawo takardun gaban kotu, aka yi musu sakin talala. An sha fadi tashi domin a yi musu shari'a amma alakalin kotun farko ya nuna cewa ba shi da hurumin yi musu shari'a domin gwamnati ce ta daukaka kara a kotun daukaka kara wato Cour d'appel, inda alkalin wannan kotun ne ya ce akwai hurumin yi wa wadannan mutanen shari'a, wadda kuma za'a yi ta a kotun karya shari'a nan gaba.

Wani mai fashin baki Dr Boukari Amadou Hassane masani a kan dokokin shari'a, a kan batun sammacin Hamma, cewa ya yi.

"Bisa harkar "Mandate direct" da ake magana, na malam Hama Amadou ne, Juju mai bincike ya kare binciken shi, kuma har an yi shari'a, ke nan yau kotu guda ne ke iya gurfanar da shi saboda yanzu, zancen fataucin yara yana kotu.

Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou

Masu fashin baki na ganin watakila a yi masa daurin talala nan gaba.

Boukari ya ce binciken da aka yi wa sauran mutanen da ke da laifin fataucin jariran haka aka yi wa Haman illa dai shi ma ya kamata ya gurfana a gaban alkalin dan ya yi masa tambayoyi, sannan daga nan ne lauyoyin na sa za su iya ajiye takardar neman masa beli.

"Shi tuhumar da ake masa, ba shi ba ne ya yi laifi shi "complice" ne an hada baki da shi, ni na yi tsammanin tuntuni, lauyoyin shi za su je su ajiye takardu a gidan yarin Filinge a kawo shi nan Yamai domin Jujun ya saurare shi, yanzu idan suka yi tambayar a ba shi sakin talala, procuror din zai sanya wadannan takardu a cikin dossiere din Haman da zarar aka gama wannan ne za a zo a yi zancen belin shi"

A kame-kamen da aka yi wa 'yan jam'iyyar Lumana Afirka wajen su 100 lokacin da suka je tarbar Hama Amadoun da ya zo sauka, sakamakon fito na fiton da suka yi da jami'an tsaro, an sako da dama daga cikinsu, yanzu saura mutane hudu, wadanda su manya ne na jam'iyyar.

Sauti da bidiyo akan labarin