Har yanzu da sauran rina a kaba wajen warware rikicin Nukiliyar kasar Iran | Labarai | DW | 13.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu da sauran rina a kaba wajen warware rikicin Nukiliyar kasar Iran

Amurka tace har yanzu tana neman hanyoyi na diplomasiyya domin warware takaddamar Nukliyar kasar Iran. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice tace Amurka ta baiyana zabin ta a fili, tana mai cewa daukacin kasashen duniya sun amince cewa wajibi ne Iran ta dakatar da shirin ta na kera makamin Nukiliya. Bayanin na Condoleezza Rice ya zo bayan wasu rahotanni dake baiyana cewa Amurka ta shirya matakan farmakin sojin akan cibiyoyin Nukiliyar na kasar Iran. Iran din dai ta baiyana cewa a yau Litinin zata cigaba da shirin ta na sarrafa sinadarin Uranium.