Har yanzu ba alamar jirgin Malesiyan na da ya bace a jiya | Labarai | DW | 08.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu ba alamar jirgin Malesiyan na da ya bace a jiya

Firaministan kasar Malesiya Najib Razak ya ce kawo yanzu ba wata alama da aka gani ta jirgin samanta da ya bace dauke da fasinjoji 239 a hanyarsa ta zuwa Beijing daga Kuala Lumpur.

Mr. Razak ya ce jami'ansu da na kasar Vietnam na aiki tukuru wajen gano jirgin saman wanda da sanyin safiyar yau Asabar jami'an rundunar sojin Vietnam, suka ce suna da yakinin cewar ya fada ne cikin teku daura da wani tsibirin mai suna Tho Chu na kasar ta Vietnam din.

Jirgin dai kirar Boeing 777 ya bace ne sa'o'i biyu bayan da ya tashi kuma galibin fasinjojin da ya ke dauke da su 'yan kasar China ne, lamarin da ya sanya mahukuntan China shiga a dama da su wajen nemo jirgin, inda suka shawarci takwarorinsu na Malesiya da su matsa kaimi wajen ganin an samo shi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman