Har yanzu ana fatali da haƙƙin ɗan Adam a duniya | Siyasa | DW | 10.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Har yanzu ana fatali da haƙƙin ɗan Adam a duniya

Shekaru 65 da ɗaukar matakin daidaita 'yancin dan Adam, matsalar dake akwai har yanzu ita ce ba a ko-ina ne a wannan duniyar ake aiwatar da dokokin kare haƙƙin ɗan Adam ba.

Tun a shekarar 1948 wani ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi bayani dalla dalla game da kare haƙƙin ɗan Adam da kuma dukkan batutuwan da suka shafi 'yanci ko wane Bani Adama a duniya baki ɗaya. Sai dai yau shekaru 65 da ɗaukar wannan mataki, matsalar dake akwai har yanzu ita ce ba a ko-ina ne a wannan duniyar ake aiwatar da dokokin kare haƙƙin ɗan Adam ba.

A sassa daban daban na wannan duniya ana fatali da haƙƙin ɗan Adam, inda a wasu wurare a fili ake keta haƙƙin ɗan Adam. Kimanin shekaru 65 bayan amincewa da ƙudurin ƙasa da ƙasa kan girmama 'yancin ɗan Adam har wannan lokaci akwai naƙasu wajen inganta wannan batu.

Ga dukkan mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam kuwa baya ga yin sara yana duban bakin gatari, dole sai ya yiwa kansa tambayar shin ta yaya za a iya shawo kan 'yan siyasa daga ƙasashen da har yanzu ake keta haƙƙin ɗan Adam, su ɗauki matakan kare haƙƙin ɗan Adam? Shin ko akwai wani alfanu a siyasance ko a zamantakewa ko ga fannin tattalin arziki, idan aka girmama haƙƙin ɗan Adam?

Markus Löning shi ne wakilin gwamnatin tarayyar Jamus a kan kare haƙƙin ɗan Adam ya ce mulki na bin doka da demokraɗiyya na inganta hulɗoɗin siyasa da na ciniki tsakanin ƙasashen duniya.

"Tun bayan da ƙasashen gabacin Turai suka fara rugunmar mulkin demokraɗiyya, dangantakarmu da ƙasashen ta inganta ƙwarai da gaske. Idan ka dubi dangantakarmu da ƙasar Poland shekaru 25 da suka gabata, za ka ga a yau Poland ta zama babbar ƙawar mu ta ƙut da ƙut."

Imke Dierßen ta kungiyar Amnesty International a nahiyar Turai ta jadadda muhimmancin dokokin kare haƙƙin ɗan Adam. Ta yi nuni da fa'idojin da aiwatar da waɗannan dokokin ke kawowa, musamman na hulɗar tattalin arziki.

"A fannin tattalin arziki ma yana da muhimmanci a girmama haƙƙin ɗan Adam. Idan kana son ka yi hulɗar ciniki da kasa kamar China, za ka ga kamfanoni na sha'awar sanin abokin hulɗarka, wato mai girmama doka, wanda kuma za a iya dogaro a kansa. Saboda haka abu ne muhimmi kamfanoni su rika ba da la'akari da kare haƙƙin ɗan Adam a ƙasashen da suke zuba jari cikinsu."

Eberhard Sandschneider masanin siyasa ne kuma daraktan cibiyar nazarin manufofin ketare na Jamus ya yi amannar cewa kare haƙƙin ɗan Adam abu ne dake tallata kansa da kansa. Sai dai ƙasashen yamma ba sa lura sosai da fa'idojinsa. Ya ce a ƙasashe da ba na yamma ba a kan ga alfanun da ke tattare da batun kare haƙƙin ɗan Adam.

"Idan aka dubi manufofin kare hakkin dan Adam a Turai, za a ga tasirin da yayi wajen daidaita lamuran siyasa. Hakan nan a kasashe dake hulda da wannan nahiya batun kare haƙƙin ɗan Adamya na samun wani matsayi mai daraja."

Sai dai a cewar masanin, manufar kare haƙƙin ɗan Adam ta gwamnatin Jamus da ma wasu ƙasashen yamma na cikin wani hali na gaba kura baya tsiyaki. A dole suna fukantar wasu ƙasashe inda gwamnatoci ke da tunani na daban game da haƙƙin ɗan Adam. Dole sai an yi takatsatsan wajen hulɗa da su, in ba haka sai a ɓata goma daya ba ta gyaru ba.

Sauti da bidiyo akan labarin