1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hanyoyin warware rikicin Afirka Ta Tsakiya

December 5, 2013

Faransa ta aike da karin sojoji 250 zuwa birnin Bangui na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1ATV7
Rebellen in Zentralafrika
Hoto: picture-alliance/dpa

Ma'akatar harkokin tsaro na Faransa ta sanar da aike wa da Sojoji 250 zuwa babban birnin Afrika ta tsakiya watau Bangui, bayan fada ya barke tsakanin tsoffin 'yan tawaye da mayakan sa kai. Kakakin ma'aikatar Gilles Jarron ya tabbatar wa taron manema labaru a birnin Paris hakan, inda kuma ya ce ana ci gaba da gwabza fada tsakanin bangarori biyun. Rahotannin kamfanin dillancin labaru na Reuters dai ya riwaito cewar mutane 23 ne suka mutu, a yayin da wasu 64 kuma suka jikkata a fadan na birnin Bangui.

A yanzu haka dai kasar ta Faransa na da yawan sojoji 650 a babban birnin kasar ta Afirka ta tsakiya, kana wasu sojoji 350 na zama cikin shirin ko ta kwana a kasar Kamaru da ke makwabtaka. Sojojin dai na daga cikin adadin dakaru 1.200 da Faransa ta shirya turawa wannan kasa da ke fama da rikicin 'yan tawaye. Tsoffin 'yan tawaye dake rike da madafun iko a Bangui dai, sun shaidar da cewar mayakan sa kai dake biyayya ga hambararren shugaba Francois Bozize sun kai musu hari. Wannan sabon fada dai ya barke ne a daidai lokacin da, Majalisar Dinkin Duniya ke shirin amincewa da kudurin Faransan na tura dakarunta kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman