Hanyoyin neman zaman lafiya ta tattaunawa | BATUTUWA | DW | 08.11.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Hanyoyin neman zaman lafiya ta tattaunawa

Zaman tattaunawa kan hanyoyin tabbatar zaman lafiya da Gidauniyar Konrad Adenauer ta Jamus ta jogoranta a garin Kaduna na Najeriya da bangarorin jama'a.

Gidauniyar Konrad Adenauer ta Jamus ta gudanar da wani taron da ya hada kan malaman adini da masu rike da sarautun gargajiya wanda kuma ya mayar da hankali kan bunkasa zaman lafiya tsakanin mabiya addinai dabam-dabam a jihar ta Kaduna.

Gidauniyar Konrad Adenauer ta yi imanin amfani da malaman addinai da masu ruwa da tsaki za su taimaka wajen ganin samar da zaman lafiya tsakanin mutane masu addinai dabam-dabam da al'adu dabam-dabam. Lokacin zaman taron an tattauna kan batutuwa masu yawa da suke hana zaman lafiya da matakan da za su taimaka na zaman lafiya tsakanin jama'a.

Sauti da bidiyo akan labarin