Hankula sun fara kwantawa a tsakanin kasashen turai bayan zaben Scotland | Labarai | DW | 19.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hankula sun fara kwantawa a tsakanin kasashen turai bayan zaben Scotland

Fargabar sake ballewar wasu yankuna daga kasashen turai, ita ce ta mamaye zaben na Scotland wacce ta nemi ballewa daga Birtaniya.

Gwama numfashi a tsakanin kasashen turai ya yi sauki a ranar Juma'ar nan, bayan da Scotland ta zabi ci gaba da kasancewa tare da Birtaniya, wani abu da ya rage fargabar sake samun wasu bangarori a wasu kasashen na turai da ke son ballewa daga iyayen gidajensu dama fargabar ficewar Birtaniyar daga kungiyar kasashen Turai ta EU.

Tuni dai Firemiya David Cameron ya bayyana farin cikinsa da ci gaba da zaman Scotland din karkashin Birtaniya kamar yadda ya ke cewa:

"Yanzu lokaci yayi na hadakan alummar daular Birtaniya mu ciyar da kasar mu gaba, a samar da daidaito da adalci ga al'ummar Scotland mafi muhimmanci ga kowane mutum na Ingila da Wales Ireland ta arewa".

Manyan birane daga kasashen na turai da dama sun shiga rudani gabannin wannan zabe, inda su ke tunanin gurbin da za a sanya Scotland din idan ta zamo kasa mai cin gashin kai cikin kungiyar ta EU da ma kungiyar tsaro ta NATO, dama fargabar masu fafutikar samun gashin kai irin su Catalonia a Spain.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo