Hana bazuwar makamai a Libiya | Labarai | DW | 02.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hana bazuwar makamai a Libiya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Libya da ta tsaurara matakai na hana bazuwar manya da kananan makamai a kasar domin magance tashin hankali.

Wani rahoto da wasu kwararru na Majalisar Dinkin Duniya suka fidda ya nuna muhimmancin da ke akwai na girka wata runduna da za ta dakile shigar da makaimai kasar ta tashoshin jiragen ruwa da ma satar danyen man kasar da ake saidawa a kasuwannin duniya.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da kasashen duniyar ke ci gaba da nuna damuwarsu sakamakon bullar reshen kungiyar nan ta IS ta 'yan jihadi a kasar ta Libiya lamarin da ake dauka a matsayin abin da ka iya ta'azzara rashin tsaron da kasar ke fama da shi.