1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Hamas na so a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Biden

August 12, 2024

Hamas ta ce babu bukatar sabuwar tattaunawa tunda bukatunta na cikin yarjejeniyar da shugaba Biden ya gabatar tun da farko.

https://p.dw.com/p/4jMgd
Shugaban Kungiyar Hamas Yahya Sinwar
Shugaban Kungiyar Hamas Yahya Sinwar Hoto: MAHMUD HAMS/AFP/Getty Images

Kungiyar Hamasda ke yaki da Isra'ila a Gaza ta bukaci masu shiga tsakani su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar maimakon kaddamar da sabuwa, wannan na zuwa ne a yayin da Falasdinawa ke tsere wa luguden wutar da Isra'ila ke yi a sassa daban-daban na Gaza.

Isra'ila ta sha alwashin yin fito-na-fito da Iran

Wannan sanarwar ta kungiyar ta Falasdinawa na zuwa ne a dai-dai lokacin da Isra'ila ta kaddamar da hari mafi muni cikin wata 10 da ya halaka mutane da dama a zirin na Gaza.

Masu neman sasanta bangarorin biyu da ke yaki da juna sun nemi a koma tattaunawa domin tsagaita wuta da aka dade ana ta nema da sakin Isra'ilawa da ke hannun Hamas.

Kasashen duniya na kira da a kawo karshen yakin Gaza

Hakan ya zo ne bayan tada kura da kisan shugabannin kungiyoyin da ke da alaka da Iran ya yi.

 Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ake gani shi ke neman tsawaita yakin saboda dalilai na siyasa ya amsa gayyatar Amurka da Qatar da kuma Masar domin tattaunawa a ranar Alhamis.