1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta nesan ta kann ta daga kungiyar al-Qaída

March 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5u

Hamas ta tsame kan ta daga kiran da kungiyar al-Qaída ta yi mata na cigaba da yakar kasar Israila. Shugaban tawagar musamman na kungiyar Hamas Kgaled Meshaal wadanda ke tattaunawa da mahukuntan kasar Rasha ya shaidawa manema labarai a birnin Mosco cewa Hamas zata baiyana matsayin ta ne bisa abin da zai amfani alúmar ta. Bayanin na Khaled Meshaal, martani ne ga jawabin da jamií na biyu mafi girma a kungiyar al-Qaída Ayman zawahiri ya yi, a wani kaset din videio da aka nuna a tashar talabijin na Aljazira dake jinjina ga nasarar da Hamas ta samu a zaben Palasdinawa. Al zawahiri ya kuma yi kira ga Hamas ka da ta amince da dukkan wata yarjejeniya da zaá kulla da Israila.