1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta maida martani ga hare-haren Isra´ila.

June 12, 2006
https://p.dw.com/p/BuuL

A cen kuwa Palestinu,a wani mataki na maida martani, dakarun Hamas sun harba rokoki 7, a ƙasar Isra´ila tunda sanhin sahiyar yau.

Bayin harin ranar juma´a da ta gabata ne,Hamas ta sanar yin watsi, da sulhun da ɓangarorin 2,su ka cimma, na tsaigata wuta , a tsawan watani 18.

A wani gefen kuma, shugaba Mahamud Abbas, ya gana da Praminsta Ismael Hanniey, da zumar cimma daidaito, a game da batun zaɓen raba gardama, da shugaban ya ambata shiryawa, ranar 26 ga wata mai kamawa.

Saidai tawagogin 2,sun watse baram baram, ba tare da cimma buri ba.

Amma,za su sake haɗuwa ranar yau litinin, domin ci gaba da tantanawa.