Hamas da Shugaban palasdinawa sun roki masu bada gudumowa su ci gaba | Labarai | DW | 31.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas da Shugaban palasdinawa sun roki masu bada gudumowa su ci gaba

Kungiyar Hamas da shugaban Palasdinawa sun roki ci gaba da bada taimako ga zuwa ga hukumar ta Palasdinawa,suna masu baiyana cewa jamaar yankin suna matukar bukatar taimako na kasashen duniya.

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya bukaci masu bada gudumowa daga nahiyar turai da su janye barazanarsu ta dakatar da bada taimakon ,wanda yace zai kara munana halin tattalin arzikin yankin wanda dama ba shi da karfi.

Wani babban jamian kungiyar Hamas kuma Ismail Hanaiye cewa yayi dukkan taimako da kasashen turai zasu baiwa hukumar palasdinawa zaayi anfani da su ne ga talakawa ba don kaiwa Israila hari ba,yace gwamnatin Hamas a shirye take a duba yadda take kashe kudadenta.